Testing

Na taba magana akan wannan kalmar ta "testing" da matasa samari ko ince wasu mazan ke amfani da shi wajen gurbata tarbiyyar ƴaƴan mutane.

Hakan kuma na taba posting din wani issue na wata baiwar Allah makamancin hakan.

Wallahi Allah maza ku ji tsoron Allah, wai namiji zai ce ma ɗiyar wani "Baby mu hadu a hotel kaza"
"baby turo mun hoton this and that".
Idan ta qi, ya gwada duk tricks dinsa abin yaci tura, sai alaji ya karkato kai "ai dama testing din ki nayi inga idan yar hannu ce ko tier leather ce".
Sannu Chef uban yan girki da zai dandana zaqin Maggi, gishiri, Onga, Mr. Chef ko knorr a abinci.
Nace ba, gidan ku da testing din, wato testing ko? .
Kwantiniyo Allah na ganinka wallahi, idan ba ka ƴaya kana da ƙannai mata. Idan aka ce za a yi testing din su ya za ka ji? Malam ka auna abin fa a ma'aunin hankali.

Ka tuba tun Mala'ikan daukar rai ba baƙunce ka ba, kana cewa ma yayan mutane testing din su ka ke.
Duk namiji mai tsoron Allah baya gwada mace ta hanyar testing, dama can sakarai ne kuma lusari. Matsa ka ban waje ni 😏😏 #ayeeshchuchuwrites

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa

TREND