A TUNANINA
A TUNANI NA
A tunani na yawan shekaru, ilimi, arziki basu ke nuna natsuwa, hankali da cikar kamalar mutum ba.
Sai kaga yaro mai karancin shekaru tattare da natsuwa, hankali da cikar kamala.
Hakan wata baiwa ce daga Ubangijin al'arsh mai girma da yake ba bayinsa ba tare da karfi ko dabarar mutum ba.
Da yawan mutane sun dauki masu karancin shekaru a matsayin wawaye da basu da 'yanci ko damar faɗin albarkacin bakinsu, hakan babban nak'asu ne a rayuwarmu. Muna manta cewa kowane ɗan Adam da irin tasa baiwar.
Duk abinda kaga Allah ya baka bafa iyawar ka ce tasa aka baka, face dai wannan nufi ne na Allah SWT.
Yan uwana matasa kar ku manta cewa kuma fa kuna da damar faɗin ra'ayinku game da harkokin rayuwa, kuna da damar tofa albarkacin bakinku. Shifa ilimi kogi ne. Kuma dokar kasa ta baku wannan damar, kamar yadda yazo a cikin tsarin constitution,shafin da ke magana akan FUNDAMENTAL RIGHT. Wanda ke nuna cewa ko wane dan kasa na da damar bayyana ra'ayin shi ( right to freedom of expression and press).
Ayeesh Chuchu✍🏾
Comments
Post a Comment