DUK TSANANI DUK WUYA!

DUK TSANANI DUK WUYA!

© Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

17-04-2018
A al'adance mace ba ta da hurumin da za ta kai karar mijinta koda kuwa ita ce ke da gaskiya, koda kuwa an ci zarafi da mutuncinta. Koda kuwa tana zaune ne cikin mawuyacin hali, al'ada ba ta bata wannan damar ba.

Dole tayi biyayya ga mijinta koda kuwa hakan ya saɓa faɗar Allah da ma'aikinSa SAW. Hakan mu ka taso kaka da kakannin ana hakan. Saboda shi miji shugaba ne, kuma shugaba baya laifi ko? Haka ake koyar da mata tun suna yaran su, ko gida akan fifita namiji sama da mace.
Tun daga kan haihuwa, idan namiji ne za a siya ma shi ƙaton gida da mota idan masu arziki ne, talaka kuwa gona ce za a bashi, a kuma yankar masa fegi a cikin gida inda zai saka matarshi. A taiƙace ma auren gata ake ma shi, ita kuma mace ko ohooo. Ita ba mutum ba ce ai, kuma ba ta zuciya a kirjinta.
Tun daga nan rashin adalci ya shiga a tsakani, cewa aka yi iyaye su yi adalci a tsakanin ƴaƴansu. Shin adalcin kenan?
Tun daga nan kun rura wutar gaba a tsakanin ƴaƴanku ba ku sani ba.
A rayuwar zamantakewa biyayya aka ce mace tayi ma mijinta shi ma din har sai idan bai saɓama dokokin Allah ba.
Amma ina! Mun taso cikin al'ada mara tushe da kan gado, mace ba ta isa ta fadi laifin mijinta ba, sai a ga kamar tayi wani gungumemen zunubi. Shin haka annabi SAW ya tafiyar da matan zamanin shi? Mata nawa ne suka kawo ƙarar mazajensu ga Manzon tsira annabin Rahama.
Akwai hadisin da ya zo cewa Khawla Bint Tha'alabah ta kawo ƙarar mijinta wajen Annabi SAW.
Wannan fa na nuna mana cewa dan mace ta kai ƙarar mijinta akan abin da take ganin zalunci ne a gare ta ba aibu bane.

Ya kamata iyaye su gane cewa ƴaƴa fa amana ce a wajen su, da mace da namiji duk daya suke a wajen Allah.
Abinda ke ban mamaki shine kullu yaumin idan mace za tayi aure itace ake ma fada, da wuya iyaye su zaunar da ɗan su su ce masa ya yi haƙurin zaman da matarshi, ya riƙa ƙokarin sauke haƙƙinta da ya rataya a wuyansa. Sai dai mi, ita mace ita ake ma wannan kashedin, saboda ita kadai Allah ya daura ma nauyin aure ko mi?

Ya kamata fa jama'a a hankalta a gane gaskiya.

Comments

Popular posts from this blog

Matan Arewa

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA

ABINDA MATA KE SO (EP1)