WANI LOKACI

WANI LOKACI

#ayeeshchuchuwrites

Bayan wani dan lokaci, radadin ya kan rage radadi. A hankali mu kan gane dalilin faruwar wasu ababen.
Mu kan fahimci dalilin da yasa suka yi hakan.
Sai dai mi? Mu kan koyi cewa ba kowa ne a rayuwar ya kan zo ya tsaya a cikinta ba har abada!

A wasu lokuttan su kan zo ne kamar taurarin cikin littafin rayuwarmu. Ba su zo dan komi ba, sai dan su koya mana wasu ababe a rayuwa, su sauya yanayin rayuwarmu,  har wani sa'in ma su koya mana yanda zamu so kanmu.
Har mu san muhimmancin da muke da shi.

Irin wadannan taurari abu ne mai wahala mu samu makwafinsu a lokacin zasu bar mu a cikin littafin rayuwarmu. Amma mi? Abu mafi muhimmancin a nan shi ne dole mu bar su su tafi, koda kuwa bamu son su tafi din.

Daga farko abin zai mana ciwo, zai nukurkushe mu.. Irin nukurkusar da za ta sa mu kasa bambamce tsakanin rana da dare.
Irin radadin da ko ina mu ka shiga yana biye da mu, yana tuna mana lokuttan da muka yi a tare masu dadi.

Wanda har ya kan sa mu rinka tunanin shin mu din kuwa masu daraja ne da muhimmanci a gare su?
Idan muna da shi mi yasa suka tafi suka bar mu?

Abu ne mai wahala mu kaucewa heartbreak!
Musamman ga mutanen da mu ka fi so. Abinda na fahimta ga rayuwar nan shine ba ka taba daura tsammaninka dari bisa dari.

Kar mu taba zaton su so mu kwatankwacin yanda muke son su.
A rayuwar nan bai zama lallai yanda kake son mutum ba ya so ka haka ba.

Abu mafi wahalar gaske idan aka zo batun rasa masoyanmu ba wai bankwana da zamu yi dasu bane, a'ah!
Tunanin yanda zamu rayu ba tare da su ba, shine abu mafi wahala a tattare da mu.

Abinda zai saurin kona mana rai bai wuce muga sun cigaba da gudanar da rayuwarsu tamkar wani abu bai faru ba, tamkar mu din wasu baki ne marasa muhimmanci a rayuwarsu.

Amma hakan ba zai sa mu manta dasu ba. Sai dai mi, matukar muna son su dole muyi hakuri, mu bar su da abinda suke ganin shine mafi kololuwar farinciki a rayuwarsu, ba dan komi ba sai dan soyayyar da muke masu.

Abin zai dame mu sosai.
Abu guda da mutane ke marari da ganin darajarsa shine wannan "Son".
  Sai mi? Abinda na fahimta da wannan rayuwar shine, kar mu je neman "So", har in mu ka je neman sa, za mu je ne dan neman magani a wajensa.
A lokacin ne zai ba mu magani na gaggawa wanda za mu ji dadi.

Sai dai kuma idan mu ka jiraye shi zai zo mana a "ba za ta", ya taho a tsabtacen shi, pure in ji bature babu gauraye.

A lokacin za mu ji a ranmu cewa ashe duniyar ba kowane lokacin ne take da zafi ba.

A wannan lokacin munyi karfin da ke tabbatar da cewa So abune mai tsabta, kuma mai wargaza lissafi, mai karya zuciya da tarwatsa rayuwar mutum.

Amma mi? A lokacin muna da wayewa ta sanin wa za mu so dan zama abokan rayuwarmu!

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa