ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY

ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY A TSAKANIN JINSI BIYU

©Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Bestie dai kalma ce da ake amfani da ita wajen nuna kimar mutum da irin matsayin da ya/ta ke da shi a zuciya, wanda a Hausance akan ce "Amini ko Aminiya", wato dai mutumin da kuke kut-kut.
Duk mutumin da za ka ba amana, ka fadawa sirrin da ke ranka, ba tare da wani dar ba. Ko kuma mutumin da a duk lokacin da wata matsala ko damuwa ta taso ma daya daga cikin su, su kan zauna su tattauna dan warware matsalolinsu, su na masu aminta da juna.
Hakan na faruwa a tsakanin jinsin namiji da namiji, mace da mace ko kuma dai wanda yanzu ake yi a zamanance wato abota tsakanin mace da namiji.
A wannan zamani da mu ke ciki an zamanantar da abun, musamman fitowar kafofin sada zumunta da kuma makarantun gaba da sakandire, inda za a samu akwai cudanya tsakanin mace da namiji.
Duk kuwa da cewa a addinance da gargajiyance babu wata alaƙa tsakanin mace da namiji da ta wuce soyayya ta aure. Sai dai mi a wannan zamani da mu ke ciki, akwai alaƙa mai karfi tsakanin mace da namiji ta abokantaka wacce mafi yawan yan boko kan kira junansu da "Bestie".
Hakan tasa nayi bincike mai zurfi akan wannan alaƙa ta "bestie", wadanne iri rawa take takawa a zamantakewa, da kuma irin matsalolin da ke tattare da ita wannan alaƙa.
A shekarar 2018 ne mujallar Social and Personal Relationships ta gabatar da bincike da tayi tun daga shekarar 2000 akan yawan daliban da ke da aminai a tsakanin ma bambanta jinsin.
Inda kiyasin ya nuna cewa kaso hamsin da bakwai (57%) ne basu da aminai a jinsin da ba nasu ba. Inda kashi arba'in da uku (43%) ne ke da aminai a jinsi da ba nasu ba.
Hakan na nuna cewa a shekaru masu zuwa watikala a iya samu daidaito, koma dai fiye da hakan a tsakanin kiyasin da aka yi.

Na tattauna da wasu daga cikin mutane, wadanda su ka hada ma masu aure da marasa aure, akan suna da "bestie", sannan ya ya suke tafiyar da ababen guda biyu, wato aboki/abokiyar rayuwa da kuma Bestie?
Akwai wadda ta bayyana mun cewa tafi aminta da namiji a matsayin amininta fiye da yar uwarta mace. Saboda za ta iya fayyace ma sa komi ba tare da ya bayyanawa duniya ba, inda ta nuna idan mace ce yar uwarta za ta iya fadawa wata, ko kuma ma tayi ma ta gori akan abin a gaba.
Wato dai hakan na nuna cewa babu sirri a tsakanin jinsin.

Sai kuma ta bakin wani bawan Allah da ya bayyana mun cewa matar da yake aure, a da bestie din shi ce. A duk lokacin da su ka samu matsala da budurwar sa, itace ke ba shi shawara. A hankali a hankali har soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su ba tare da sun farga ba, wadda ta kai su ga auren juna.

Na ji ta bakin wani magidanci da ya bayyana mun cewa "Ina da kawar da duk wani sirri nawa ta sani, ta sanni fiye da matata. Ko a waya nayi magana idan ina cikin damuwa tana ganewa. Idan na samu matsala da matata ita ke nusar da ni. Ta dalilinta na san halayyar mata sosai. Sai dai matsalar matata kullum tunaninta soyayya ce ke tsakanin mu, hakan na haifar da rashin jituwa a tsakanin mu. Har wayata ta taba fasawa saboda besty ta".

Wani bawan Allah yace "A gaskiya wannan alaka ta Bestie kan iya rikidewa ta zama soyayya, amma dai ya danganta da yanda kuke kusanci da juna.
A bangarena, babu abinda ke tsakanina da besty ta mace sai hulda rayuwa ta yau da kullum, zan iya fada miki yanda ta sanni ta san matsalolina wacce nake so ba ta sanni ba, shawara ko wacce iri ce za ta bani, a wasu lokuttan idan muka samu sabani da wacce nake so itace mediator tsakanin mu, wacce nake so ta san ta haka zalika ita ma bestyta ta san wacce nake so.
Haka kuma wacce nake so tana da wanda yake shine bestyn ta, abokin karatun ta ne, komi za su yi tare suke yi, kuma muddin yaga tana abinda bai dace ba zai ma ta magana, idan ya mata fada a kan wani abu da take yi wanda be dace ba taki bari, sai kira ni ya fada mun don inyi ma ta magana,muna yawan tattaunawa da shi kamar yanda ita ma suke mutunci da hira da bestyta.
Amma fa daga ranar da mu ka yi aure to maganar besy ta kare sai dai kuma mutunci wanda ba za a rasa ba, Bestie ta dole za ta hakura, shi ma kuma dole zai hakura. Amma a yanzu gaskiya bana jin wani abu mara dadi dan macen da nake so da kauna tana da besty sai dai idan ita dauke shi a matsayin wani abu daban".

Ta wani bangaren kuma ga abinda wani yace "Zama bestie ai soyayya ne, kamar ace ne a hada shayin da suga bai ji ba da wanda ya ji suga. Wato dai soyayya ce a fakaice wadda ke da naƙasu ta wadansu bangarori da ba zasu iya kaiwa ayi aure ba. Misali rashin kudi ko asali, addini da kuma shekaru. Kinga duk wadannan zasu iya kawo naƙasu, daga nan sai a fake da bestie".

Wasu na ganin abota da wani jinsin na da alfanu ga rayuwar mutum, wasu kuma na ganin hakan sam bai dace, musamman idan aka yi duba da addini da kuma al'ada ba a san wani abu wai shi amintaka ba tsakanin mace da namiji wanda ya wuce aure.

Zamu duba kadan daga cikin alfanun dake cikin wannan abota duba da ra'ayoyin jama'a akan hakan.

-Taimakawa wajen fahimtar kowane jinsi
  Masana sun bayyana cewa abota tsakanin ma bambanta jinsi kan sa bangarorin guda biyu su fahimci junansu. Saboda abota ta hada su, babu karya ko sauya wasu halaye a tattare da kowane jinsi, kowane daga cikin su kan tsaya a yanda yake ba tare da ya canza ba.
Wanda a soyayya ba haka bane, a kan samu kowane na kokarin ganin ya boye wani hali mara kyau da yake da shi.
Inda abota tsakanin Bestie kuma abin ba haka bane, kowane na nuna tsagwaron halinsa ne ba tare da ya boye wani abu ba. Ta hakan ne ake samun fahimtar juna sosai a tsakanin kowane jinsi.

-Rike sirri
  Kamar yadda na bayyana a farko, wadanda ke abota da jinsin da ba nasu ba, sun fi samun kwanciyar hankali wajen fayyace sirrikansu hankali kwance ba tare da sun ji wani dar-dar ba na tunanin wani ko wata zai bayyana sirrin su. Akwai amintaka mai karfi a tsakaninsu

-Bada shawara
Kowannen su na kokarin ganin ya bada shawara mai kyau wajen warware wata matsala da daya ya shiga. Su kan auna abin a ma'aunin idan su abin ya faru a kansu.
Sannan a kan abubuwan da suka shafi masoya, su kan bada shawara idan wata matsala ta kunne kasancewar su ba jinsi daya ba, kowane ya san yanda ake shawo kan jinsin sa.
Misali mace tayi fada da saurayinta, besty dinta kan zauna ya ba ta shawarar yanda za ta jawo hankalin saurayinta kasancewar shi namiji ya san yanda halayyar maza ta ke.

-Rage radadin rashin aboki/abokiyar rayuwa

  Masana sun nuna cewa abota da jinsin da ba na ka kan rage radadin rashin masoyi ko masoyiyya wato wadanda ke "single" a turance. Saboda kowane bangare na kokarin ganin ya rage ma dan uwansa kadaici, ta hanyar fira da tattaunawa wasu abubuwa da suka shafi rayuwa.

Kadan kenan daga cikin alfanun Bestie ga masu yi.

Rashin alfanun sun hada da

-Kowa zai tunanin kuna son juna
A addini da kuma al'ada babu mai yarda da cewa wai wata abota ce a tsakanin ku. Kowa tunaninsa shine soyayya ce a tsakanin ku, ta hakanne kuma zaku iya rasa masoya na asali.

-Kawo hargitsi a tsakanin masoya
Ba kowane masoyi zai yarda a ce budurwarsa ko matarsa na da abokin da take bayyanawa duk matsalolinta a wajen shi. Haka ta bangaren mata ma, ba wacce za ta so a ce mijinta na da wata da suke matukar kusanci da juna, wadda ta san mijinta fiye da ita. Hakan ba karamin hargitsi yake kawowa ba, saboda zargi zai shiga tsakani.
A tunanina babu abotar da ta wuce ta tsakanin masoya, ta hakan ne zai sa ku fahimci juna sosai. Ba tare da third party ya shigo ciki ba.

-Bangaren iyaye
Babu iyayen da za su so ace diyar su nada aboki namiji, ba ma zasu yarda ba. Dan tunanin su zai karkata akan cewa soyayya ce tsakani, wanda ta hakan sai su matsa lamba akan a fito ayi maganar aur saboda su a tunanin su ai soyayya ce ta hada ku.

Kadan kenan daga binciken da nayi akan besty, wasu na ganin alfanun shi a zamantakewar su, wasu na ganin rashin alfanun shi, wanda shine ya ci karo da addini da kuma al'ada.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa