Supportive Saurayi/Miji

Da yawan mata na son supportive boyfriend/husband.. Ba wai kowane lokaci za kai ta I love you I love you ba.. A wasu lokuttan ma ko ka fada ba zata yi tasiri ba. Ba koda yaushe ne tatsuniya ina so da mararinki ke tasiri ba.
All she needs is ka nuna ma ta son a aikace ba a baki ba. Ka ba ta duk wata gudunmuwa da kake gani za ta taimaka ma ta a rayuwa wajen cikar burin ta.
Someone like Rafeeah za ta so wanda zai supporting business dinta, zai rika bombarding dinta da ideas. Zai taimaka ma ta wajen ganin ta cigaba a rayuwa, he will be there for her through the thick and thin.. No matter what ba za ta manta da shi ba, saboda ya nuna soyayyar shi a aikace.
🤣 🤣 Kamar Amierah ce ka ba ta kayan girki, books na girke-girke wadanda za ta karu dasu, maybe ka ba ta idea on yanda zata juya cooking skills dinta into business.. Kullum kana yabawa da kwarzanta.

Someone like Gatawa da Naseeba hada su poetry books Malam ka ga aiki, 🤣🤣Ko yane ka nuna jin dadinka a poems dinsu. Kace Mairo rera mun peom din nan taki mai dan karen dadi. Why not ki kirkiro da kaza da kaza, kafin ka sani sai ka ga kunyi plan tare, saboda ka nuna kana son cigabanta.

Duk macen da ke da talents na wani abu tana son namijin da zai karfafa ma ta gwiwa, zai tsaya tsayin daka wajen ganin cigabanta. Ko a ina yake zai bugi kirji cewa wannan matata ce ko budurwa ta ce and I'm proud of her.
Amma Malam kai kullum ba ka da magana sai ta ina kaunar ki, ina son ki zama uwar yayanah. Ah ah ! Ai dole a gaji to abu ne da kullum ta saba ji, har ta fara zaton ma shirgo ta kake.

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker #thefragiletable

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa