MAI SONKI

Idan kina cikin relationship amma kin kasa gane kan relationship din take a break. Kar ki zauna cikin relationship din da za ki zauna cikin kunci, ya zama kina tare da partner dinki ne dan kar a ce ba ki da saurayi ko wani abu.
Take break! ☹☹
Ki huta da zama cikin kunci, yafi maki da zama cikin relationship din da ba zai amfana ma ki komi ba.
Believe me yafi maki da tara yawan samarin da ba wanda kike so babu wanda kike tunanin yana kawo farin ciki a rayuwar ki.
Gara ki zauna single, kiyi ta addu'ar Allah ya zaba ma ki mafi alkhairi. Kafin ki sani sai ki ga Mr. Love mai PhD a love a ya danno.

Zai zo a lokacin da ba ki taba tsammani ba, ke da kanki za ki ji cewa he is the one.
Zai ba ki dukkan soyayyar da kike bukata saboda dama you're meant for each other.

Sannan zai fahimce ki musamman idan yasan relationships dinki na baya sun taba zuciyar ki, zai ba ki lokaci ki fahimci kanki, zai ba ki duk wani support da kike bukata. Ba zai taba takura ma ki akan a dole sai kin so shi a lokacin ba.
Zai zamo abokinki na kut da kut. Matukar kuna son gina soyayya ingantacciyar dole sai kun zamo abokan juna, ta hanyar hakan ne zamu yarda da junanku. Saboda abota a soyayya na daga cikin tubalin da ake gina soyayya a kanta.
Kowa zai zama shine babu karya babu boye-boye babu yaudara.

A kullum burin shi ya ga kin zama mutumiyar kwarai. Ba kuma zai nuna ma ki kyama ko tsangwama ba, a'a zai taro ki ne ta hanya mafi sauki wacce bama za ki gane he is complaining about your habits ba. Sannu a hankali he will make you a better person da mutanen da ke tare da ke zasu gane hakan...

Idan har wanda kike tare da shi nada kwatanta biyu ko uku ko makamancin hakan ki tabbatar ma kanki cewa kinyi dace. Idan kuwa babu ko guda a ciki 🙄🙄 gara ki tattara yanaki yanaki ki kara gaba.. Duk relationship din da za ki ji cewa ba ki farin ciki da shi kina jin kamar baki da partner barin shi yafi ma ki. Aure ba wai je ki ki dawo bane, abu ne da ake tunanin idan anyi shi to ya zama har gaban abada!
Please don’t settle for just anything, aim high, because you deserve the best. Keep being you! 😍

Ayeesh Chuchu
19-03-2018

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa