Cigaba Da Rayuwa

💔💔💔

Cigaba da rayuwa bayan rabuwa da masoyi abu ne mai tsayawa a rai da matukar wahala.
Musamman idan rabuwar ta zo a lokacin da ake ganiyar son juna. A lokacin da mutum ya daura burikan rayuwar shi a kan masoyinsa.
Amma a hankali a hankali radadin da zafin ke tafiya.
A hankali za ka fahimci dalilinsu na rabuwa da kai. 
Learn that ba fa kowa da ka hadu da shi ne zai zauna da kai har karshen rayuwa. Sometimes kamar taurarin fina-finai suke zuwa don su koya ma wani darasi a rayuwa, su nuna ma wani bangare na rayuwa da ba ka taba experiencing ba. They will teach you how to love yourself and know your worth! 
Wasu daga cikinsu abu ne mawuyaci ka maida gurbin su,abu ne mai matukar wahala da karya zuciya ka bar su su tafi a lokacin da suke da muradin barin rayuwarka.
Amma mi? Ba yanda ka iya, dole ka bar su su tafi koda ba ka so, ko da hakan na nufin karyewar zuciyar ka, you have to let them go ðŸ˜©....

A farko rabuwar ku, rabuwa ce da za ta bar ka cikin wani irin yanayi maras dadi.
Akwai lokacin kai kadai za ka sha kukanka ka koshi, bacci ya gagari idanunka, koda baccin ya dauke ka za ka farka da mafarkin sun dawo cikin rayuwarka.
Abun za ka gan shi tamkar a mafarki.
Kai ne bibiyar rayuwarsu, karanta text messages da chats dinku.
Kana jin kamar za ka wayi su dawo su ce ma wasa suke. Sai dai mi? Duk wanda ya furta rabuwa a gare ka, baya da sauran wani matsugunni ko gurbi da yayi saura a rayuwar ka.
Na san ba abu bane mai sauki.
Heartbreak is inevitable! ðŸ’” especially with the people you love. 
Muna tunanin zasu so mu kamar yanda muke sonsu, wanda hakan ba gaskiya bane. Ba mu da ragamar jan akalar rayuwar su.
Sun zabi su rabu da mu a lokacin da muka fi bukatar su. Bai zama lalle abinda kake ji game da wani ba, ya zama tilas shi ma ya ji hakan.

Abu mafi ciwo a rabuwa bai wai bankwana bane ba, a’a ka koyi rayuwa ba tare da su ba, abu mai ciwo shine ka ga sun cigaba da rayuwar su tamkar ba ku taba rayuwa tare ba, sam rabuwar ba ta dame su ba. Honestly you can’t blame them.
Saboda abinda suka zaba kenan.
Ya rage naka ka samama kanka mafita.
Na sani ba abu bane mai sauki.
Amma mi, duk wani abu da kasan yake tattare da kai da zai iya tuna ma dasu kauda shi.
Goge texts, chats da duk wani abu da ya shafe su.
 Kai daure ka bar bibiyar rayuwarsu da sama ma kanka soyayya da farinciki da kanka.

Kayi kokarin yin abinda zai kawo ma natsuwa, ta hanyar yin abubuwan da zasu dauke ma hankali.

#ayeeshchuchuwrites

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE