INA MAFITA?
"Lami! Lami!! Lami!!!".
"Na'am Inna".
"Ina ki ka shige ne? Sai kwala ma ki kira nake?".
"Bitar karatun da akai mana a makaranta nake yi".
"To yi maza ki siyo man gishiri goma, manja na hamsin da ajino na talatin shagon Audu. Kar fa ki tsaya wasa".
"To Inna".
Cikin azama ta amshi kuɗin ta fita daga gidan.
***
"Lami ke ce da ranar nan?".
"Eh! Inna ta aiko ni".
"Shigo cikin shagon mana kin tsaya daga waje kamar wata baƙuwa".
"A'a sauri Inna tace inyi kar in dade".
"Ba ki son in ba ki alawar kenan? Yau harda Naira goma zan ƙara ma ki".
"Ni dai a'a".
Fitowa yayi daga shagon, ya duba hanya yaga babu mai tahowa, yasa hannu ya kinkimi Lami yarinya yar kimanin shekara bakwai.
"ka bari, ban so, zafi yake mun".
Jikinta na ta kyarma kamar ana kaɗa mazari gab! Gab!! Gab!!! Ya shige da ita cikin shagon,be ɓata lokaci ba wajen haiƙe ma ta.
Ta na gunjin kuka yasa tsumma ya toshe ma ta baki. Sai da ya gama biyan buƙatarsa sannan ya kyale ta. Ya kwance ma ta bakin da ya kulle,tsumman yasa ya goge jinin da ke jikin Lami.
"Idan ki ka sake na ji kin faɗi wannan maganar ga wani, sai na sa wannan wuƙar na kashe ki, na kashe iyayenki".
Ya sa wuƙar a setin wuyanta.
Ta gama tsorata matuƙa gaya, zufa ta karyo ma ta ta ko'ina ta na fitar da numfashi cikin sauri kamar wacce tayi tseren gudu.
Ta kaɗa kanta kamar wata ƙadangaruwa.
Ya miƙa ma ta kayan da aka aike ta, tare da Naira goma da alawa.
***
A hankali take tafiya tare da bubbuɗa ƙafafu, saboda irin zogin da al'aurarta ke ma ta har ta isa gida.
"Lami tun ɗazu da na aike ki sai yanzu ki ka ga damar dawowa? Bayan sai da na faɗi ma ki kar ki tsaya wasa a hanya ko?".
"Inna ya fita ne sai da na tsaya ya dawo".
"Ba ki zuwa bakin titi ko dole sai wajen Audu?". Ta fizgi kayan ta shige madafi.
"Ki zo ki mun jajjage, ga kayan miyan can na ajiye kusa da turmi".
Da kyar ta miƙe tana dafa bango.
"Inna nan wajen ke mun zafi".
"Ba ki tashi ƙorafin ba ki lafiya sai kinga an sa ki aiki. Da ba ni na haife ki ba Lami sai ace takura ma ki nake yi".
"Da gaske nake Inna".
Ba ta ko kalli Lamin ba ta cigaba da harkokin gabanta.
***
"Lami zo nan?"
"Duk irin faɗan da nake ma ki ba ki ji ko? Ban hana ki shiga banɗaki ba buta ba?".
"Ka hana ni Baba, zafi nake ji idan nayi tsarki".
"Asabe zo ki duba yarinyar nan, ni sam kwana biyun nan ban yarda da lafiyarta ba. Ya za'a yi haka kawai ka ji zafin yin tsarki tunda ba barkono aka zuba a butar ba".
"Ka san halin Lami da ƙorafin tsiya, ciwo kadan ta kama raki, tun rannan take man wannan zancen, bamma bi ta kanta ba, dan lambo ne irin na Lami, ba ta son moriya".
"Ni dai idan kin ji tawa ki duba ta, idan ta kama har asibiti a duba lafiyarta".
"Shikenan gara aje asibitin dai tunda ta nace da rakin".
"Ga ɗari uku idan za'a siya magani, ni na fita".
ASIBITI
"Lami Ɗantani".
Ta ja hannun Lami su ka shiga ofishin likita.
Bayan ƴan tambayoyi da akai ma Lami, mahaifiyarta na taya ta amsa wasu.
Jim kadan! Ma'aikaciyar jinya ta shigo sanye da fararen kayanta.
"Sista Jummai duba al'aurar wannan yarinyar ki ga mi ke damunta".
Nan aka daura Lami saman wani gado mai faɗi da yafi kama da teburi.
Bayan sun dau tsayin mintuna da aƙalla zasu yi goma sha.
Sista Jummai ta fara salati da salallami.
"Lami tashi zaune, faɗa mun waya taɓa sa ma ki hannu a nan?".
Kuka ta hau yi.
"Ba kowa".
"Ki faɗa man inada jakkar alewa har da kyautar Naira hamsin zan ma ki".
Cikin zumuɗi fa fara magana.
"Ba Audu bane yake sa mun hannu da wani abu a nan. Yace kar in faɗawa kowa".
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ya lalata man ɗiyata".
"Malama kiyi haƙuri mu yi duk wani bincike da zamu yi. Dole sai anyi gwaje-gwaje waɗanda zasu tabbatar da zargin da ake yi. Tunda yanzu alamu ne su ka bayyana. Sai an ba Lami gado dan tana buƙatar kulawa".
"Ni dai aban ɗiyata mu tafi, asirin mu a rufe ba tare da kowa ya ji ba. Yanzu duk wanda ya ji fyaɗe akai ma Lami ai ya zama abin gori a gareta har girmanta,ta zo ta rasa mijin aure".
"Yanzu kin gwammace ki rufa ma wanda ya tozarta rayuwar ɗiyarki asiri dan kawai kada ya zama abin surutu akan ƴancin ɗiyarki?".
"Wai miya ruwanki ne? Ɗiyata ce, iyakar ku duba lafiyarta shikenan. Dan haka aban ɗiyata mu tafi, magani ma za'a yi ma ta na gargajiya".
***
"Asabe! Kin cuci rayuwar yarinyar nan, duk irin faɗi tashin da malaman jijyar nan suka yi sai da ki ka watsa ma su ƙasa a ido. To ni dai ba da yawuna ba,ina fa jin irin jan hankalin iyaye da ake yi a rediyo akan irin wannan matsalar, sannan inyi shiru. Dole a ƙwato ma Lami ƴancinta,ƙila ma ba ita kadai ba ce ba".
"Malam kayi haƙuri a rufe maganar nan, yanzu gari zai dauka, ni baƙincikina ai ta kallon Lami da abun, gara mu yi shiru a ne ma ma ta magani na gida asirin mu rufe".
"Tsaya ki ji, ni ba za'a yi wannan jahilcin da ni ba. Kinga tafiya ta ofishin ƴan sanda. Ai idan nayi shiru na cuci Lami, ɗan ba ki jin rediyo ne shiyasa, amma ko da zan ƙarar da dukiyata sai na tabbatar da an hukunta Audu".
Fuuuu ya ja takalmansa ya fita daga gidan.
Asabe ta yi jugum! Abin duniya duk ya dame ta.
OFISHIN ƳAN SANDA
"Yanzu ka tabbatar da cewa shi ya yi ma ƴar ka fyaɗe?".
"Kwarai da gaske Yallaɓai, na tabbatar ba za ta ma sa ƙarya ba. Kuma ga katin asibiti da su ka tabbatar da fyaɗe akai ma ta".
Sun rubuta koken da Malam Ɗantani ya kawo, aka haɗa shi da ƴan sanda zuwa shagon Audu.
***
Isar su ke da wuya su ka iske Audu na rufe shagonsa.
"Assalamu Alaikum"
"Wa alaikumus Salam".
"Muna buƙatar ganin ka a caji ofis yanzu".
"Mi nayi?".
"Idan mun je ka gani".
Su ka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota da mahaifin Lami ke ciki.
Bayan sun isa caji ofis, ƴan sanda su ka tuhumi Audu akan zargin da ake ma sa.
"Wallahi ƙarya ake man ni ban san wata Lami ba".
Nan su ka buƙaci Ɗantani ya je gida ya taho da iyalinsa, shi ma Audu aka tura gidansu.
***
"Ɗantani kayi haƙuri a rufe maganar nan iyakar ta ofishin ƴan sanda, tunda da aminci a tsakanin mu. Abin kunya ne mutane su ji wannan labarin".
"Abin kunya? Shi Audu be san abin kunya ba ya haiƙe ma yarinya ƙarama kamar Lami. Idan ka ga na yi shiru a maganar nan an bi ma Lami haƙƙinta ne".
"Idan kuɗi ka ke so kayi magana ni mai ba ka ne a rufe maganar, su ma ƴan sandan in ba su na su kason".
"Ai idan na amshi kuɗinka na ci amanar Lami. Duk irin faɗakarwa da ake yi a gidajen rediyo kullum ina jin irin wannan matsalolin sai in kasa daukar mataki".
BAYAN KWANA BIYU
Malam Ɗantani ya shigar da ƙara kotu, duk irin yanda iyayen Audu da matarsa su ka so ya haƙura su sasanta a tsakanin su ya ƙi.
Duk bayanan da aka gabatar da shaidu sun nuna Audu ne ya ma Lami fyaɗe, tare da jerin yara sa'anninta aƙalla za su kai biyar. Haka yake ribatar su da alewa tare da kuɗi.
Kotu ta yanke ma sa hukuncin da aka tanadar ma ma su irin halin Audu.
***
"Wayyo Allah! Audu zafi, zan mutu".
Ta kwalla wata ƙara mai razanarwa.
"Lami tashi ba Audu ba ne, ni ce".
Asabe ta yi tagumi, abin duniya ya dame ta. Tunda abin nan ya faru Lami ke firgita, ta rage yawan kazar-kazar.
Shigowar mai gidan yasa ta saki ajiyar zuciya.
"Malam ina ga a sake maida Lami asibiti, na gaji da firgitar da take yawan yi".
"Ai ga irin ta nan, malaman jinyar nan na iya bakin ƙokarinsu ki ka hana su, dama irin wannan abu su ke gudu, fatana ma kada yawan firgitar da take yi ya shafar ma ta kwakwalwa. Audu ya cuce mu wallahi".
"Ai sai dai Allah ya saka mana, tun a duniya sai ya gani. Sai yanzu na ji daɗin kama shi da akayi. Duk surutun mutane be dame ni ba, lafiyar ɗiyata shi yafi man komi".
"Sai yanzu ki ka san da haka?".
"A bar tone-tone Malam, mu tafi asibitin da ita, a duba ta".
Wannan abu ne dake faruwa sosai a society, abun takaici mutum yayi wa jikar sa fyade. Allah ya kyauta.
ReplyDelete