Posts

BIN YAN TSIBBU

Image
BIN YAN TSIBBU   Abin mamaki da takaici ne a ce mace na bin bokaye don ta mallaki namiji. Abin ban haushi da takaici yanda abin ya zama ruwan dare a tsakanin ƴan mata yanzu.   To ke Jummala tun yanzu ba ki yi auren ba kin fara bin bokaye don a karkato ma ki da zuciyar shi, ina ga anyi auren ai sai abinda yayi gaba. Shin kin gwammace ki siyar da Aljannarki saboda namiji?  Ki zo ki aure shi ba kwanciyar hankali, kinga kin zo duniya a zero za ki koma a zero. Ki lura, ki kuma hankalta bin bokaye ba zai kai ki ko'ina ba face ga halaka, saboda imaninki tunin kin zubar da shi, kin kasa yarda da cewa Allah shi ke komi.   Mi zai hana ki tashi ki roki Allah tsakiyar dare a lokacin da wasu daga cikin bayinSa ke bacci ki kai ma Sa kukanki kina mai imani da yaƙinin cewa shi zai amsa ma ki addu'ar ki, ya biya ma ki bukatar ki. Abin da yafi daga mun hankali bai wuce yanda wasu ke bin bokaye da Malamam tsibbu ba fa dan su auri saurayi suke bin su ba, sai dan wata bi...

RASHIN YABAWA

Image
RASHIN YABAWA Yana daya daga cikin ababen da ke kawo rikici a zamantakewar ma'aurata rashin yabawa. Miji na iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kyautatawa matarsa sai a samu akasi ita sam ba ta ganin kokarin sa, duk abinda yayi sai ta kawo inda ba'a kyauta ma ta ba. Wanda hakan shi ke sa daga baya mazan su zame hannayensu a harkokin iyalinsu. Duk inda namiji yake bai fa son a raina kokarin sa, koda kuwa a zahirance ba haka abin yake ba, yafi son a kambama sai yaji dadi ya kara himma. Haka kuma a fannin mata, mace na iya bakin kokarinta wajen kyautata ma namiji, amma shi a wajen sa ba abinda take yi. Idan girki ta yi sai ya samu inda aka yi kuskure, nan zai hau sababi, ba ya tunanin ba fa kullum take wannan kuskuren ba, miyasa ba zai fahimce ta ba. Daga nan an dauko makaman wargaza ingantacciyar alaka, tun kowa na yi dan a kyautata ma juna daga karshe sai a daina. Kowa ya koma yin abinda yaga dama, abinda yaga zai iya. Da haka yara ke tasowa abinda suka ga iyayen su nayi s...

TIMABEE

Image
FATIMA BABAKURA (TEEMABEE) Matashiyar yar kasuwa Mai sana'ar hada jakkunan hannu (handbags) na mata. Fatima Babakura wadda aka fi sani da TEEMABEE, matashiyar budurwa mai aƙalla shekaru ashirin da biyu. Tayi karatun degree ɗinta na farko a jami'ar Mcmaster University Canada. Ta fara sana'ar hada jaka ne a shekarar 2013, inda ta fara zanawa a takarda. Daga nan ne ta tsunduma ka'in da na'in wajen haɗa jakkunan hannu na mata. Fatima Babakura na daya daga cikin matasa mata masu kaifin basira da hazaƙa. Wadanda suka kara fito da martabar yan Afrika a idanun duniya. Mace mai kananan shekaru wadda ta fito daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya abin a jinjina ma ta ne. Ta fitar da samfur na jakkuna da yawa daga shekarar 2013, ta siyar dasu ga mutanen dake wajen Kasar Canada kama da Dubai, London, South Africa, USA da sauran shagunan siyar da kaya dake a Canada. Babban burin Fatima bai wuce ta ga ta gina katafen kamfani a Nijeriya ba, wanda ba zai tsaya a iya jakku...

SANNU BA TA HANA ZUWA

Image
SANNU BA TA HANA ZUWA   AYEESH CHUCHU   Ya kai ɗan uwana , ka ganta kana so koh? Kana son aurenta , kana son ta zama uwar ya'yanka koh?   Idan har kana son ta haura waɗannan matakai , sai ka bi a hankali , kar ka yi garaje . Sai ka fahimci wacece wadda ka ke son ta taka waɗannan matakai . Shin ka san wacece ita ? Mi ya ja ra'ayinka ka ji kana sonta ? Wadanne halaye suke burge ka a tattare da ita ? Shin iliminta da wayewarta (ba wayewar 'yan bariki ba) sun ma ka ? Shin ka taɓa cin karo da wani hali na ta mara kyau ? Wanda ka ke jin za ka iya zama da ita . Shin ita ɗin ka ke so? Ko kuwa wani abu na ta. Shin kana tunanin za ta iya ba ya'yanka tarbiyyar da ta dace? Shin ita ɗin ka taɓa cin karo bacin ranta ko a lokacin da take cikin bakinciki ? Ta ya kake tunanin za ka iya shawo kanta a irin wannan yanayi ? Shin za ka iya canza wasu daga cikin dabi'unta wa...

AISHA AUGIE KUTA

Image
AISHA AUGIE KUTA An haifi Aisha Augie a garin Zaria, a ranar 11th April, 1980. Ɗiya ce ga marigayi   Sanata Adamu Baba Augie da Justice  Amina Adamu. Ta yi aure tana da yara uku maza.   Ta yi karatun digiri ɗinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta karanci fannin Mass Communication. Inda ta ke Masters ɗinta a bangaren Media and Communication a jami'ar Pan African University da ke Lagos.  Aisha Augie kwararriyar mai daukar hoto ce, wanda hakan ya samo asali daga kyautar kyamara (camera) da mahaifinta ya ma ta.  Abin mamaki ne a Nijeriya kuma yankin Arewa a ga mace na daukar hoto, sai dai a wajen Aisha Augie daukar hoto abu ne da ta dade tana sha'awar yi.  Aisha Augie mace ce da ta jajirce wajen ganin cigaban yara mata da kuma matasa baki daya. Ta kasance mai bada gudunmuwa a harkokin da suka shafi yara mata, dalilin hakan ne ma UNICEF ta rantsar da ita a matsayin "High Level Women Advocate on Education with a focus ...

UMM ZAKIYYAH

Image
UMM ZAKIYYAH   An haifi Umm Zakiyyah a shekarar 1975, a Long Island dake ƙasar New York. Kafin a haife ta iyayenta mabiya addinin Kirista ne, Mahaifiyarta mai suna Delores Moore da mahaifinta Clark sun musulunta ne ana dauke da cikin Umm Zakiyyah. Ita ce ɗiya ta farko da aka haifa cikin musulunci a gidansu, inda aka sa ma ta suna "BAIYINAH". Umm Zakiyyah ta kashe mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubucen maƙala, rubutun waƙe a jaridu. Zamanta ɗaliba a jami'ar Emory da ke a Atlanta ta ƙasar Georgia. Ta sadaukar da mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubuce a jaridar da makarantar su ke fitarwa ta ɗalibai. A shekarar 1997 ta kammala karatunta na digiri, inda ta fito da kwalin digiri a bangaren BA. Elementary Education. Daga nan ta fito a matsayin Marubuciya, Malama kuma mai bada darussa akan al'amuran rayuwa. A shekarar 2001 ne ta fitar da littafinta na farko mai sunan IF I SHOULD SPEAK, littafin da ya ƙara fito da baiwar da Allah ya ...

LALE MARHABIN

Image
Lale marhabin da zuwan wannan rana Ranar da garin Makka ya haskaka Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Zarah Duk mai son Ɗaha ya so ahalinSa Miji ga Khadijatu, angon Aishatu Amini ga Abubakar Saddiqu Siriki ga Aliyu ɗan abi Talib Zuwan Ɗaha duniya ta haskaka Ya kawo mana hanyar shiriya  Domin tsira a gobe ƙiyama Muna ma su Haske da walwali Ɗaha ya zo mana da littafi  Wanda anka kira da Qur'ani Saƙo daga sarkin sarakuna Allah mabuwayi gagara misali   Ɗaha mai kira zuwa ga tauhidi  Domin tsira  a hawan siraɗi Ɗaha masoyi ga al'ummarsa Ya roƙi salama ga al'ummarsa Mu so Manzonmu mai dubun falala  Kyawawan halayen Ɗaha sun yawaita  Duk wanda ya yi koyi da shi ya rabauta  Kowa ya ƙi Ɗaha ya kafirta  Lale marhabin da wannan rana  Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Al-Qaseem Kaka ga Hassan da Hussaini Ya Allah ka dado tsira  Ga Manzonka mai farar aniya Don shi anka ƙ...