SON ABIN DUNIYA

SON ABIN DUNIYA A TSAKANIN ƳAƳA MATA Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Muna cikin wani zamani da matuƙar za'a samu abin duniya to idanun kan rufe ne ta kowane hali domin samun cikar buri. Hakan yasa mata ma ba'a bar su a baya ba, wajen ganin sun sami abin duniya ta kowane hali. Wannan ya samo asali ne daga rashin wadatacciyar zuciya na wasu daga cikin mata, musamman ma ƴan mata a wannan zamanin. Har ta kai ta kawo mace kan iya zubar da ƙima da mutuncinta wajen ganin ta sami abin duniya. Akwai abubuwan da ke jawo son abin duniya ga ƴaƴa mata wanda sun sha faruwa kuma suna kan faruwar. Kadan daga cikinsu sun haɗa da: -Rashin cusawa yara tsoron Allah, daga inda yaro ya tashi ba a cusa masa tsoron Allah ba a duk inda yake, to tabbas dole a samu matsala. Wannan tsoron Allah ne zai taimakawa yaro a duk inda yake iyaye basu da shakku akansa, saboda duk abinda zayyi zai tuna da cewa Allah da ya halicce shi na kallonsa. Hakan take a wajen ...