BIN YAN TSIBBU

BIN YAN TSIBBU Abin mamaki da takaici ne a ce mace na bin bokaye don ta mallaki namiji. Abin ban haushi da takaici yanda abin ya zama ruwan dare a tsakanin ƴan mata yanzu. To ke Jummala tun yanzu ba ki yi auren ba kin fara bin bokaye don a karkato ma ki da zuciyar shi, ina ga anyi auren ai sai abinda yayi gaba. Shin kin gwammace ki siyar da Aljannarki saboda namiji? Ki zo ki aure shi ba kwanciyar hankali, kinga kin zo duniya a zero za ki koma a zero. Ki lura, ki kuma hankalta bin bokaye ba zai kai ki ko'ina ba face ga halaka, saboda imaninki tunin kin zubar da shi, kin kasa yarda da cewa Allah shi ke komi. Mi zai hana ki tashi ki roki Allah tsakiyar dare a lokacin da wasu daga cikin bayinSa ke bacci ki kai ma Sa kukanki kina mai imani da yaƙinin cewa shi zai amsa ma ki addu'ar ki, ya biya ma ki bukatar ki. Abin da yafi daga mun hankali bai wuce yanda wasu ke bin bokaye da Malamam tsibbu ba fa dan su auri saurayi suke bin su ba, sai dan wata bi...