Posts

Showing posts from July, 2018

A TUNANINA

A TUNANI NA A tunani na yawan shekaru, ilimi, arziki basu ke nuna natsuwa, hankali da cikar kamalar mutum ba.    Sai kaga yaro mai karancin shekaru tattare da natsuwa, hankali da cikar kamala.   Hakan wata baiwa ce daga Ubangijin al'arsh mai girma da yake ba bayinsa ba tare da karfi ko dabarar mutum ba.   Da yawan mutane sun dauki masu karancin shekaru a matsayin wawaye da basu da 'yanci ko damar faɗin albarkacin bakinsu, hakan babban nak'asu ne a rayuwarmu. Muna manta cewa kowane ɗan Adam da irin tasa baiwar.   Duk abinda kaga Allah ya baka bafa iyawar ka ce tasa aka baka, face dai wannan nufi ne na Allah SWT.   Yan uwana matasa kar ku manta cewa kuma fa kuna da damar faɗin ra'ayinku game da harkokin rayuwa, kuna da damar tofa albarkacin bakinku. Shifa ilimi kogi ne. Kuma dokar kasa ta baku wannan damar, kamar yadda yazo a cikin tsarin constitution,shafin da ke magana akan FUNDAMENTAL RIGHT. Wanda ke nuna cewa ko wane dan kasa na da damar bayyana ra'ayin shi

RABUWAR IYAYE

RABUWAR IYAYE Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com 11-07-2018 Muna cikin wani zamani da auri saki ya yawaita a tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai masu karfi da ke assasa mutuwar aure. Sai dai mi? Mutuwar auren na kawo matsaloli a rayuwar yaran da ke tsakanin ma'auratan. A irin wannan zamanin da mu ke ciki, iyaye ma na tare suna bakin kokarin wajen tarbiyyantar da ƴaƴansu ana samun matsaloli ina ga iyayen da suka rabu da juna. Da yawan yaran hankulan su na rabuwa ne gida biyu, su kan rasa shakuwa ta iyaye da ƴaƴansu musamman idan daya daga cikin iyayen ke tare da ƴaƴan, kunga kenan sun rasa shakuwa ta daya bangaren.    Matuwar aure a tsakanin iyaye na jawo rashin yarda a tsakanin yaran, zasu riƙa kallon iyayen ta wata fuska ta daban, ana samun masu nuna ƙyayya ga daya daga cikin iyayensu saboda dalilinsu na ganin cewa watakila uban ne ya assasa rabuwarsu da mahaifiyarsu, ko kuma ta bangaren ita mahaifiyar ce musabbabin hakan. Wasu daga cikin yaran basu samun kulawar