Posts

MAI SONKI

Idan kina cikin relationship amma kin kasa gane kan relationship din take a break. Kar ki zauna cikin relationship din da za ki zauna cikin kunci, ya zama kina tare da partner dinki ne dan kar a ce ba ki da saurayi ko wani abu. Take break! ☹☹ Ki huta da zama cikin kunci, yafi maki da zama cikin relationship din da ba zai amfana ma ki komi ba. Believe me yafi maki da tara yawan samarin da ba wanda kike so babu wanda kike tunanin yana kawo farin ciki a rayuwar ki. Gara ki zauna single, kiyi ta addu'ar Allah ya zaba ma ki mafi alkhairi. Kafin ki sani sai ki ga Mr. Love mai PhD a love a ya danno. Zai zo a lokacin da ba ki taba tsammani ba, ke da kanki za ki ji cewa he is the one. Zai ba ki dukkan soyayyar da kike bukata saboda dama you're meant for each other. Sannan zai fahimce ki musamman idan yasan relationships dinki na baya sun taba zuciyar ki, zai ba ki lokaci ki fahimci kanki, zai ba ki duk wani support da kike bukata. Ba zai taba takura ma ki akan a dole sai kin s...

Supportive Saurayi/Miji

Da yawan mata na son supportive boyfriend/husband.. Ba wai kowane lokaci za kai ta I love you I love you ba.. A wasu lokuttan ma ko ka fada ba zata yi tasiri ba. Ba koda yaushe ne tatsuniya ina so da mararinki ke tasiri ba. All she needs is ka nuna ma ta son a aikace ba a baki ba. Ka ba ta duk wata gudunmuwa da kake gani za ta taimaka ma ta a rayuwa wajen cikar burin ta. Someone like Rafeeah za ta so wanda zai supporting business dinta, zai rika bombarding dinta da ideas. Zai taimaka ma ta wajen ganin ta cigaba a rayuwa, he will be there for her through the thick and thin.. No matter what ba za ta manta da shi ba, saboda ya nuna soyayyar shi a aikace. 🤣 🤣 Kamar Amierah ce ka ba ta kayan girki, books na girke-girke wadanda za ta karu dasu, maybe ka ba ta idea on yanda zata juya cooking skills dinta into business.. Kullum kana yabawa da kwarzanta. Someone like Gatawa da Naseeba hada su poetry books Malam ka ga aiki, 🤣🤣Ko yane ka nuna ji...

DEAR WOMEN

Image
DEAR WOMEN   🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀Na ma rasa ta ina zan fara abubuwa ne cinkus a raina kuma batun na mata ne, some may not be happy with the write-up but I don't give a damn. My dear ladies know your worth, soyayya fa ba hauka bace. Ki natsu! Ki kama sauran mutuncin da ya saura ma ki. Kar soyayya ta kai ki ta baro ki, wai ace ki tura nude pictures dan kawai yana ce ma ki "Baby I love you".. I love you banza da wofi, akwai I love you din da ta wuce ki kama mutuncinki. Wai har kina da guts na fadin Kar yace baya son ki to shi din kanin ubanki? Idan yace ba ki son shi sai mi? Ya kara gaba da ma ke ba sonki yake ba. Abinda yake son gani da sanin yanda yake tayi hakuri a daura har sai ya gaji da gani 🙄.. No man in this world worth your nude pictures, no man ina fada ma ki. Koda sadaki ya ajiye da lefe baida wannan hurumi, don't even think of trying it. Idan ba haka ba ki kuka da kanki. Duk ranar da taku ta hado ku ranar z...

#FreePadsForGirls

#FreePadsForGirls Ina ta samun sakonni akan kamfen dinmu na #FreePadsForGirls, da yawa sun nuna farincikinsu da kuma goyon bayan su akan kamfen din. Alal hakika abu ne mai muhimmanci mu haɗa hannu wajen ganin wannan kamfen ya isa ga jami'an gwamnati. Ba dole sai pads din nan sun zama kyauta ba, a'a akalla ace dai an rage kaso mafi tsoka na farashinsu. Da yawan iyaye ba lallai bane su san muhimmancinsa ga ƴaƴa mata, sannan su iyaye ma ta ba kasafai mazajensu ke siya masu ba, sai fa mazaje yan boko da ke sako shi a provision. Yaran talakawa kuwa musamman na kauyuka ba ta pad iyayen suke ba, ta ya ya za'a ci abinci suke yi. Idan muka yi duba da package guda na Virony sanitary pad 700 - 800 yake, wane uba ne a kauye zai cire 800 ya siya pad ga yarinya daya, yana ganin wannan ya isa ya siya kwanon abinci ko zaman teburin mai shayi. Sannan akwai matsalar da yawa yaran nan basu san yadda za su yi amfani da pads din ba, basu san yanda za su kula da kansu ba. Rashin menstru...

TREND

Chuchu and LubnaSufyan calmlubna@gmail.com ayeeshasadeeq2010@gmail.com TREND Akwai abinda turawa kan kira 'TREND' da za'a iya fassarawa da wani abu sabo da zai shigo ko ince 'YAYI'. Kamar sabuwar shadda da samari zasu dinga yayi, burin kowanne a ciki ya mallaka, machine da makamantansu. A wajen mata kamar turare, dinki ko wani abu daya danganci kwalliya, wannan TREND bai tsaya a iya abubuwan amfani ba, har da wakoki ko finafinai da zasu shigo yan yayi. TREND dinmu na yau ta bangaren wakokine, wakokin da kan zo da salon rawa kala-kala. A shigowar 2018 din nan anyo wakoki kala-kala irin su Shaku-shaku, Kope challenge ga kuma sabuwa yar yayi wai ita collapse challenge Wadannnan kalolin rawa da su ka zo da rawar da burin kowanne matashi ko matashiya su saka wakar su kwaikwayi rawar. Ok! ba sai addini ya kai ga shigowa ciki ba, bara mu taba al'ada kamun muzo kan addini, akwai raye rayen da a al'ada ta malam Bahaushe ko namijin bai kamata ya yi ta ba balle h...

KASUWANCIN ZAMANI

Image
Sannu a hankali na gane cewa smartphones ba wai dan kayi chats kadai ne amfanin su ba. You can use smartphone to advertise your business, ba wai a social media kadai ba. Google is very helpful when it comes to network marketing business, akwai Google My business wanda za ka iya amfani da shi wajen tallata kasuwancinka free. But what is need most shine content na page dinka. Misali na shiga Google kawai na rubuta Ayeesh Chuchu a search engine, duk wani abu da ke dauke da Ayeesh Chuchu zai bayyana a search results dinka. Maybe wani na neman wani abu, kamar a ce ya yi searching "bakery in Katsina". Ace ka/ki na sana'ar bakery, already Kuna da sites a Internet. Wannan search engine din zai tattaro dukka bakeries da ke Katsina wadanda ke internet. Sannan zai zabo wadanda ke da contents mai kyau. Anan amfanin content ya shigo. Kun ga kenan hakan zai iya taimakawa wajen bunkasa kasuwancinku. Abinda yasa nayi wannan maganar shine I got a customer through Google my business ...

DA SAURAN RINA A KABA

RANAR MATAN KARKARA TA DUNIYA DA SAURAN RINA A KABA Ayeesh A. Sadeeq ayeeshasadeeq2010@gmail.com Idan aka yi la'akari da yanayin da matan karkara ke ciki bana tunanin an samu wani cigaba na azo a gani ba. Musamman idan aka yi duba da yawaitar kananan yara dake qara fantsama a cikin harkar nan ta tallace-tallace. Wadannan ƙananan yara mata sune ake jefawa cikin halin ha'ula'i, musamman yawaitar cin zarafin su da ake yi nayi masu fyaɗe, yara ƙanana ana samun su dauke da cikin shege a dalilin haiƙe masu da ake yi, ko kuma da ra'ayin kansu ta hanyar yi masu romon baka. Su fa mutanen karkara ba kasafai suke kallon gidajen talabijin ba, karanta jaridu da kuma sauraron Radiyo. Babbar hanyar da ya kamata a bi wajen wayar masu da kai bai wuce ta hanyar community outreach. Wannan kira ne na musamman ga kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka a wajen ganin an rage mafi yawa daga cikin kason matsalolin da ake samu a karkara. Ta fannin tallace-tallace da ƙananan ya...