Posts

DEAR WOMEN

Image
DEAR WOMEN   🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀Na ma rasa ta ina zan fara abubuwa ne cinkus a raina kuma batun na mata ne, some may not be happy with the write-up but I don't give a damn. My dear ladies know your worth, soyayya fa ba hauka bace. Ki natsu! Ki kama sauran mutuncin da ya saura ma ki. Kar soyayya ta kai ki ta baro ki, wai ace ki tura nude pictures dan kawai yana ce ma ki "Baby I love you".. I love you banza da wofi, akwai I love you din da ta wuce ki kama mutuncinki. Wai har kina da guts na fadin Kar yace baya son ki to shi din kanin ubanki? Idan yace ba ki son shi sai mi? Ya kara gaba da ma ke ba sonki yake ba. Abinda yake son gani da sanin yanda yake tayi hakuri a daura har sai ya gaji da gani 🙄.. No man in this world worth your nude pictures, no man ina fada ma ki. Koda sadaki ya ajiye da lefe baida wannan hurumi, don't even think of trying it. Idan ba haka ba ki kuka da kanki. Duk ranar da taku ta hado ku ranar z...

#FreePadsForGirls

#FreePadsForGirls Ina ta samun sakonni akan kamfen dinmu na #FreePadsForGirls, da yawa sun nuna farincikinsu da kuma goyon bayan su akan kamfen din. Alal hakika abu ne mai muhimmanci mu haɗa hannu wajen ganin wannan kamfen ya isa ga jami'an gwamnati. Ba dole sai pads din nan sun zama kyauta ba, a'a akalla ace dai an rage kaso mafi tsoka na farashinsu. Da yawan iyaye ba lallai bane su san muhimmancinsa ga ƴaƴa mata, sannan su iyaye ma ta ba kasafai mazajensu ke siya masu ba, sai fa mazaje yan boko da ke sako shi a provision. Yaran talakawa kuwa musamman na kauyuka ba ta pad iyayen suke ba, ta ya ya za'a ci abinci suke yi. Idan muka yi duba da package guda na Virony sanitary pad 700 - 800 yake, wane uba ne a kauye zai cire 800 ya siya pad ga yarinya daya, yana ganin wannan ya isa ya siya kwanon abinci ko zaman teburin mai shayi. Sannan akwai matsalar da yawa yaran nan basu san yadda za su yi amfani da pads din ba, basu san yanda za su kula da kansu ba. Rashin menstru...

TREND

Chuchu and LubnaSufyan calmlubna@gmail.com ayeeshasadeeq2010@gmail.com TREND Akwai abinda turawa kan kira 'TREND' da za'a iya fassarawa da wani abu sabo da zai shigo ko ince 'YAYI'. Kamar sabuwar shadda da samari zasu dinga yayi, burin kowanne a ciki ya mallaka, machine da makamantansu. A wajen mata kamar turare, dinki ko wani abu daya danganci kwalliya, wannan TREND bai tsaya a iya abubuwan amfani ba, har da wakoki ko finafinai da zasu shigo yan yayi. TREND dinmu na yau ta bangaren wakokine, wakokin da kan zo da salon rawa kala-kala. A shigowar 2018 din nan anyo wakoki kala-kala irin su Shaku-shaku, Kope challenge ga kuma sabuwa yar yayi wai ita collapse challenge Wadannnan kalolin rawa da su ka zo da rawar da burin kowanne matashi ko matashiya su saka wakar su kwaikwayi rawar. Ok! ba sai addini ya kai ga shigowa ciki ba, bara mu taba al'ada kamun muzo kan addini, akwai raye rayen da a al'ada ta malam Bahaushe ko namijin bai kamata ya yi ta ba balle h...

KASUWANCIN ZAMANI

Image
Sannu a hankali na gane cewa smartphones ba wai dan kayi chats kadai ne amfanin su ba. You can use smartphone to advertise your business, ba wai a social media kadai ba. Google is very helpful when it comes to network marketing business, akwai Google My business wanda za ka iya amfani da shi wajen tallata kasuwancinka free. But what is need most shine content na page dinka. Misali na shiga Google kawai na rubuta Ayeesh Chuchu a search engine, duk wani abu da ke dauke da Ayeesh Chuchu zai bayyana a search results dinka. Maybe wani na neman wani abu, kamar a ce ya yi searching "bakery in Katsina". Ace ka/ki na sana'ar bakery, already Kuna da sites a Internet. Wannan search engine din zai tattaro dukka bakeries da ke Katsina wadanda ke internet. Sannan zai zabo wadanda ke da contents mai kyau. Anan amfanin content ya shigo. Kun ga kenan hakan zai iya taimakawa wajen bunkasa kasuwancinku. Abinda yasa nayi wannan maganar shine I got a customer through Google my business ...

DA SAURAN RINA A KABA

RANAR MATAN KARKARA TA DUNIYA DA SAURAN RINA A KABA Ayeesh A. Sadeeq ayeeshasadeeq2010@gmail.com Idan aka yi la'akari da yanayin da matan karkara ke ciki bana tunanin an samu wani cigaba na azo a gani ba. Musamman idan aka yi duba da yawaitar kananan yara dake qara fantsama a cikin harkar nan ta tallace-tallace. Wadannan ƙananan yara mata sune ake jefawa cikin halin ha'ula'i, musamman yawaitar cin zarafin su da ake yi nayi masu fyaɗe, yara ƙanana ana samun su dauke da cikin shege a dalilin haiƙe masu da ake yi, ko kuma da ra'ayin kansu ta hanyar yi masu romon baka. Su fa mutanen karkara ba kasafai suke kallon gidajen talabijin ba, karanta jaridu da kuma sauraron Radiyo. Babbar hanyar da ya kamata a bi wajen wayar masu da kai bai wuce ta hanyar community outreach. Wannan kira ne na musamman ga kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka a wajen ganin an rage mafi yawa daga cikin kason matsalolin da ake samu a karkara. Ta fannin tallace-tallace da ƙananan ya...

YOU CAN HAVE YOUR ROMANTIC DINNER DATE, A TSAKAR GIDAN KU GARI YAYI DUHU.. TAURARI SUN HASKA SARARIN SAMANIYA ..

Image
Money Money Money! Yes! We all love Money. Babu wanda zai ce bai son kudi, ko a ce wane ko wance kun cika son duniya. Muna son duniyar nan to the extend of wasunmu ma na mantawa da dalilin halittarsu a doron kasa. Wasunmu na mantawa da akwai Lahira.. 😂 So kar kace mun ba ka son kudi, I love Money🙈.. Amma mi? Kudi ba zasu zama number one priority din mu a rayuwa ba, a ce komi zamu gina muna gina shi ne based on money.. That's so bad.. Har ta kai relationships dinmu muna gina su saboda kudi. Mostly mu mata anan muke fadawa halaka da juyin juya halin rayuwa. Ban manta ba someone sent me a message "Wai ke kina yi kamar ba ki son kudi waya san mi kike yi".... Murmushi nayi kawai. Tabbas! Ina son kudi, shiyasa ma na daga dacewar in neme su da kaina, zan fi ganin value din su... Mafi yawan mata na da burin auren mai kudi, ni fa banga laifin su ba. Laifin su daya, da suka sa kudin gaba da komi. Mata nawa ke auren masu kudin amma ba su da kwanciyar ...

YAUDARA

YAUDARA Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Na dade ina son inyi magana akan wannan maudu'in amma ban san ta ina zan fara ba, ataikace sai na fara typing sai in rasa abin rubutawa ba wai dan ban san mi zan rubuta, sai dan yadda maudu'in ke da sarkakiya, ta yanda nake son ya kasance balance ta kowane bangare. A kullum yaumin ina son in ja hankalin yan uwana matasa maza da mata da mu ji tsoron Allah mu kuma kyautata niyyar mu akan duk abinda muka sa a gaba. A kwanan nan na ji cases da basu kirguwa akan wane ya yaudari wance, wance ta yaudari wane. Shin mi muke so mu zama ne? Duniyar nan idan ka ji wasu abubuwan da ke faruwa sai ka ji mutanen kansu na sure ma ka, soyayyar ma na fita daga ranka, saboda amana tayi karanci. Duniyar ta zamo so scary. A nawa tunanin da ra'ayin banga amfanin soyayyar da ba za ta kai ku ga aure ba, to don mi za ku yi ta bayan kun san ba auren juna za ku yi ba, yafi tun farko kar ku samo abinda ku ka san ba za ku iya karasa shi ba. Kace...