Posts

ABINDA MATA KE SO (EP1)

ABINDA MATA KE SO EP1 A mafi yawan lokutta maza kan yi ta korafin “wai ku mata mi kuke so ne?”  “Ba a iya ma ku”... “Ba a birge ku”... Bla bla bla.... Har yanzu ba ku fahimci mi mata ke so ba, har wasu kanyi tunanin ba a birge mace ko wani abu makamancin haka. A duk inda mace take tana son namijin da zai rika motivating dinta.  Ba wai ka zo ka zama motivational speaker ba😂.. Man! Wannan maganar motivation a relationship na ke magana a kai. Every woman wants a man that can inspires her, wanda zai iya taimaka ma ta a duk lokacin da ta bukaci haka.. Akwai lokuttan da mace za ta riski kanta cikin wani hali na damuwa da bakinciki, a wannan lokacin tafi bukatarka. A lokacin za ka iya lallashin ta da misalai maybe wadanda ma suka faru a kanka, ka nuna ma ta za ta iya wuce wannan wajen . Za ta iya zama kalar macen da take son zama.. Idan ta rasa wannan wajen ka, nan fa bestie ke shigowa, coz he will be there for her , he’ll cheer her up.. Zai ji matsalolin ta zai b...

Matan Arewa

Okkkayyy! Dan anyi maganar kishiya kun fi kowa tada jijiyan wuya. Kece "wayyo Allah, ka cuce ka yaudare ni".. Kwana biyu kuma ki fara "ai ta gama mallake shi".   I'm fed up with "arewa women are not romantic".. Ya tura dan SMS na kara jadadda soyayyar shi a gare ki. Duk rawar ganin da yayi, you can't even reply with "I love you" idan wahalar typing kike. Yasan kin gani kin kuma yaba. Haba! Kiyi laifi ba za ki ce "sorry" ba. Ya yi ma ki kyauta babu "Thank you". Da kin haihu shi kenan ya zama Baban Indo, dan wasa da hirar soyayya kunyi bankwana da su. Da anyi magana ki ce yara. Ko kin girma da haka. In za ki fita kin iya kwalliya da kashe dauri, da kin dawo gida kin kama yawo da zani da shirt, ko daurin kirji. Dare nayi ki haye gado shi kenan. Kin ajiye ma Baban Indo abinci, ya ci ko kar yaci ke dai ai kin girka. Tsakanin ki da mijin ki sai dai maganar kudi "A bani kudin cefane, a bani kudin ankon bik...

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. A wannan zamani da mu ke ciki aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa su ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar wannan kalubale. Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai suka iske abun ba haka bane. Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita ciki...

DALILAI DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI

DALILAI SHA DAYA DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI Kwanakin baya nayi ta samu korafi daga bakin mata su na kawo kokensu akan miskilan maza. Da yawa na takaicin halayyar irin wadannan mazaje saboda dabi'arsu ta nuna halin ko in kula. Duk da an san cewa dabi'ar mata ce yawan magana, babban rauninsu a rayuwa shine "So", sabili da emotional side dinsu. Inda a maza ba hakan bane, kamar yadda na karanta a cikin littafin "Men are from Mars, Women from Venus", inda na gane bambance-bambance da ke tsakanin mace da namiji. Wasu na ganin cewa miskilanci ra'ayi ne, wani bangaren kuma na ganin halitta ce. Akwai taken da Bahaushe yayi ma miskili "Kafi mahaukaci ban haushi". Ana kallon miskilin mutum a kan cewa mutum ne shi mai girman kai, da jiji da kai, mutum mai wulakanci wanda sam ba haka bane ba. Yanayin halittar shi ce haka ta rashin son magana da kuma shiga abinda bai shafe su ba. Alal hakika ba'a fahimci ya rayuwar miskili take ba, shiyasa da y...

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

ALAMOMI GOMA DAKE NUNA CEWA SOYAYYA TA KARE TSAKANIN KI DA SHI Akwai bambanci tsakanin namiji na sonki da kuma bai sonki, wanda zai nuna hakan a aikace, a baki da kuma yanayin mu'amalar ki da shi. Da yawan mata za su fara tunanin ko nayi wani laifi ne? Miye dalilin canzawar shi? Mi ya kamata inyi wajen kara karkato da hankalin shi a gare ni? Ire-iren wadannan tambayoyi ne da za su yi ta yawo a zuciyar budurwar da ta rasa gane kan saurayinta. Wata ba za ta fahimci cewa sonta ne ya daina ba, sai ta fara neman sasanci, ta shiga halin damuwa da tashin hankali musamman idan aka yi sa'ar cewa ta mutu a soyayyar sa. A matsayinki ta mace, wacce aka sani da rauni musamman a bangaren soyayya, ya zama wajibi ki natsu ba'a shiga soyayya ta ka, kin san mi kike so game da namiji sannan ki san alamun da ke nuni da cewa wannan yaudara ce ko kuma an daina yayinki, saboda mune a mafi yawan lokutta muke fadawa ciki. Monica Parikh dake a NYC masaniya akan zamantakewa da soyayya ta bayyan...

Phone Calls

A wannan zamanin da mu ke ciki, daga lokacin da soyayya ta kullu tsakanin mace da namiji sai ku ga yawan phone calls ya qaru, a bangaren mace za ta yi ta jin dadi ai wane na matukar sona. Har labari za ta rika ba qawayenta "wallahi a rana sai muyi waya sau goma da shi, sama da 30mins ko 1hr". As time goes on, Sai ya rage kiran nan, maybe a rana sau hudu-biyar. Daga nan sai ta fara sama ranta ai ya fara kula wata, before you know ta fara korafi shi kenan fitinar yau daban ta gobe daban, kafin kace mi duk an ishi juna within 2 months. Da kin tambaya "wance ina wane?" "ke kyale ni da shi, dan rainin wayau ne bama tare yanzu".. Next month wani sabon bf ne.. Shima kuma haka. Miyasa a zamanin da ba'a samun wadannan matsalolin? Coz firarsu ta gani ga ga ki ce, koma minene a faifai za a kasa ayi ta ta kare. Duk wata doguwar firar waya rage karsashin soyayya take, make your phone calls short. Kuyi ta magana ba coma ba fullstop, tun ana fadin gaskiya ha...

ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY

ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY A TSAKANIN JINSI BIYU ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Bestie dai kalma ce da ake amfani da ita wajen nuna kimar mutum da irin matsayin da ya/ta ke da shi a zuciya, wanda a Hausance akan ce "Amini ko Aminiya", wato dai mutumin da kuke kut-kut. Duk mutumin da za ka ba amana, ka fadawa sirrin da ke ranka, ba tare da wani dar ba. Ko kuma mutumin da a duk lokacin da wata matsala ko damuwa ta taso ma daya daga cikin su, su kan zauna su tattauna dan warware matsalolinsu, su na masu aminta da juna. Hakan na faruwa a tsakanin jinsin namiji da namiji, mace da mace ko kuma dai wanda yanzu ake yi a zamanance wato abota tsakanin mace da namiji. A wannan zamani da mu ke ciki an zamanantar da abun, musamman fitowar kafofin sada zumunta da kuma makarantun gaba da sakandire, inda za a samu akwai cudanya tsakanin mace da namiji. Duk kuwa da cewa a addinance da gargajiyance babu wata alaÆ™a tsakanin mace da namiji da ta wuce soyayya ta aure. Sai d...