MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA
MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. A wannan zamani da mu ke ciki aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa su ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar wannan kalubale. Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai suka iske abun ba haka bane. Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita ciki...