ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY
ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY A TSAKANIN JINSI BIYU ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Bestie dai kalma ce da ake amfani da ita wajen nuna kimar mutum da irin matsayin da ya/ta ke da shi a zuciya, wanda a Hausance akan ce "Amini ko Aminiya", wato dai mutumin da kuke kut-kut. Duk mutumin da za ka ba amana, ka fadawa sirrin da ke ranka, ba tare da wani dar ba. Ko kuma mutumin da a duk lokacin da wata matsala ko damuwa ta taso ma daya daga cikin su, su kan zauna su tattauna dan warware matsalolinsu, su na masu aminta da juna. Hakan na faruwa a tsakanin jinsin namiji da namiji, mace da mace ko kuma dai wanda yanzu ake yi a zamanance wato abota tsakanin mace da namiji. A wannan zamani da mu ke ciki an zamanantar da abun, musamman fitowar kafofin sada zumunta da kuma makarantun gaba da sakandire, inda za a samu akwai cudanya tsakanin mace da namiji. Duk kuwa da cewa a addinance da gargajiyance babu wata alaƙa tsakanin mace da namiji da ta wuce soyayya ta aure. Sai d...