SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATASA

SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATASA Ayeesh A. Sadeeq 27-06-2018 ayeeshasadeeq2010@gmail.com Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin matasan wannan zamanin, abin al'ajabi da mamaki bai wuce yanda gaba daya jinsin wato maza da mata ke tu'ammali da kayan maye. Da yawan su hakan ya faro asali ne daga abokan da su ke mu'amala da su. Mafi yawancin iyaye da malamai na matukar kokari wajen ganin sun nuna ma matasa illar da ke tattare da shaye-shaye. Sai dai akan yi rashin sa'a da wasu iyayen da ke bada gudunmuwarsu wajen lalacewar yaransu. A matsayinmu na matasa akwai buƙatar mu san wadanne abokai ya kamata mu yi hulda da su, kamar yadda bature ke cewa "Show me your friends and I'll tell you who you are". Wasu zasu taso da kyakkyawar tarbiyya, sai dai kash! Abokan da suke haduwa dasu kan gurbata wannan kyakkyawar tarbiyya. Akwai matsalar nan ta da yawan iyaye basu damu da sanin abokanan ƴaƴansu ba, idan aka yi rashin sa'a sai yaran su hadu da abokanan ...