LOKACI Kowane dan Adam yana da lokacinsa na wanzuwar abubuwa a cikin rayuwarsa. Wani kan gama karatu da wuri ya kere ma sa'oinsa, wani ya samu aiki da wuri, wani yayi aure da wuri da sauran ababe makamantan hakan. Haka kuma kowa da tasa ƙaddarar a rayuwa, taka daban haka kuma tawa ƙaddarar daban, abin da ake so dai mutum ya yarda da kowace irin ƙaddara walau mai kyau ko akasin haka. Mutane kan yi kuskuren fahimtar waye kai da kuma abokinka, ta iya yiwuwa abokinka, dan uwanka ko makwabcinka ya riga ka samun nasara a rayuwa, ya samu shahara cikin ƙanƙanin lokaci amma kai shiru kamar an shuka dussa. Mutane zasu danganta ka da marar nasara a rayuwa ko wani wanda ya gaza samun nasara. Sun manta cewa kai da shi ba hanyarku ɗaya ba, ba kwazonku ɗaya, ba haka aka ƙaddaro ma ku ba, kuna da bambamci. Kowanen ku nada tsarin ta sa rayuwar. Kadan daga cikin mutane ne zasu yi hakurin ganin cigabanka, wasu zasu yi ma dariya wasu ...