AISHA AUGIE KUTA

AISHA AUGIE KUTA An haifi Aisha Augie a garin Zaria, a ranar 11th April, 1980. Ɗiya ce ga marigayi Sanata Adamu Baba Augie da Justice Amina Adamu. Ta yi aure tana da yara uku maza. Ta yi karatun digiri ɗinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta karanci fannin Mass Communication. Inda ta ke Masters ɗinta a bangaren Media and Communication a jami'ar Pan African University da ke Lagos. Aisha Augie kwararriyar mai daukar hoto ce, wanda hakan ya samo asali daga kyautar kyamara (camera) da mahaifinta ya ma ta. Abin mamaki ne a Nijeriya kuma yankin Arewa a ga mace na daukar hoto, sai dai a wajen Aisha Augie daukar hoto abu ne da ta dade tana sha'awar yi. Aisha Augie mace ce da ta jajirce wajen ganin cigaban yara mata da kuma matasa baki daya. Ta kasance mai bada gudunmuwa a harkokin da suka shafi yara mata, dalilin hakan ne ma UNICEF ta rantsar da ita a matsayin "High Level Women Advocate on Education with a focus ...