SAI MAZA SUN CANZA

SAI MAZA SUN CANZA! © AYEESH CHUCHU ayeeshasadeeq2010@gmail.com A wannan zamanin da mu ke ciki rayuwar aure ta zama wata irin bahaguwar rayuwa, wadda akan kasa gane kanta a wasu lokuttan. Maza kune Allah ya ba ragamar jan akalar gidajenku, ku ne shuwagabanni masu mulkin alƙaryar gidajensu. Hakan ya zama abin tutiya, nuna iko da isa a cikin alƙaryarku. Har wasu kan yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da mulkin kama karya a cikin gidajensu. Dukkanku za ku tsayu gaban Allah a ranar gobe ƙiyama kuna q nannaɗe acikin sarƙa har sai kun tsira daga kun sauke haƙƙin da Allah ya rataya a wuyanku na iyalanku. Ba'a ba ku wannan mulkin ba face dan kun kasance marasa rauni,amma kadan daga ciki ne ke kwatanta adalci a tsakanin su da iyalansu. A wannan zamanin ne da mu ke ciki miji da Allah ya daura ma nauyin iyalinshi be damu da su ba, kullum cikin fita yake ya nemo amma hakan be sa ya sauke nauyin da ya rataya akansa ba. Wani ya tafi ya bar matar da ...