WA ZAN AURA?
WA ZAN AURA??? ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Wannan ce tambayar da ke zuwa a zukatan wadanda ba su yi aure walau mace ko namiji. Muna cikin zamanin da competition ya yi yawa,saboda yawan competition ɗin sai ya zamo muna manta abubuwa ma su muhimmanci da ya kamata mu duba kafin a yi aure, burinmu dai ayi auren dan wance ko wane ya yi, ko dan sha'awa da makamantansu wanda at long last we end up in the wrong hand,ko kuma auren yaƙi zuwa ko'ina. Aure ba abin wasa bane, ba kuma je ka dawo ba ne, ana Fatan idan anyi aure ya zama har abada,mutuwa kadai za ta raba wannan auren. Rashin nazari da kuma tantance abinda ya dace da mutum a yayin neman aure babban matsala ce, yana daga cikin ummul aba'isin da mafi yawan auren da ake yi basu zuwa ko ina. Saboda rashin dace a cikin aure ba abinda bai haifarwa, yana iya illata rayuwar mutum gaba daya. Da yawan mutane sun yi aure amma su na jin ina ma za su dawo ...