Posts

Cigaba Da Rayuwa

💔💔💔 Cigaba da rayuwa bayan rabuwa da masoyi abu ne mai tsayawa a rai da matukar wahala. Musamman idan rabuwar ta zo a lokacin da ake ganiyar son juna. A lokacin da mutum ya daura burikan rayuwar shi a kan masoyinsa. Amma a hankali a hankali radadin da zafin ke tafiya. A hankali za ka fahimci dalilinsu na rabuwa da kai.  Learn that ba fa kowa da ka hadu da shi ne zai zauna da kai har karshen rayuwa. Sometimes kamar taurarin fina-finai suke zuwa don su koya ma wani darasi a rayuwa, su nuna ma wani bangare na rayuwa da ba ka taba experiencing ba. They will teach you how to love yourself and know your worth!  Wasu daga cikinsu abu ne mawuyaci ka maida gurbin su,abu ne mai matukar wahala da karya zuciya ka bar su su tafi a lokacin da suke da muradin barin rayuwarka. Amma mi? Ba yanda ka iya, dole ka bar su su tafi koda ba ka so, ko da hakan na nufin karyewar zuciyar ka, you have to let them go  😩 .... A farko rabuwar ku, rabuwa ce da za ta bar ka cikin wani irin yan

ABINDA MATA KE SO (ep2)

ABINDA MATA KE SO EP2 Mata na son namijin da ke da sense of humor. Wanda idan abin dariya ya kama zasu yi dariyarsu tare. Wanda zasu yi wasa ba tare da jin shakku ko dardar na cewa zai dau abin personal. Aa tana son wanda idan ta tsokane shi, shi ma zai taya ta tsokanar. Ba namijin da za ta kalla kullum daga maganar “I love you”, sai fa wani serious abu. Shi kullum bai san wasa..  Baya sa son wasa, yana forming elder elder... Baabaa baya son raini...  We want someone that both of us can be stupid together.. Relationship da mutumin da bai da sense of humor akwai matsala... Kullum magana daya ce, har sai kin gaji da ita. Shi fa sam baya son abinda za ki raina shi. #ayeeshchuchuwrites #tableshaker

ABINDA MATA KE SO (EP1)

ABINDA MATA KE SO EP1 A mafi yawan lokutta maza kan yi ta korafin “wai ku mata mi kuke so ne?”  “Ba a iya ma ku”... “Ba a birge ku”... Bla bla bla.... Har yanzu ba ku fahimci mi mata ke so ba, har wasu kanyi tunanin ba a birge mace ko wani abu makamancin haka. A duk inda mace take tana son namijin da zai rika motivating dinta.  Ba wai ka zo ka zama motivational speaker ba😂.. Man! Wannan maganar motivation a relationship na ke magana a kai. Every woman wants a man that can inspires her, wanda zai iya taimaka ma ta a duk lokacin da ta bukaci haka.. Akwai lokuttan da mace za ta riski kanta cikin wani hali na damuwa da bakinciki, a wannan lokacin tafi bukatarka. A lokacin za ka iya lallashin ta da misalai maybe wadanda ma suka faru a kanka, ka nuna ma ta za ta iya wuce wannan wajen . Za ta iya zama kalar macen da take son zama.. Idan ta rasa wannan wajen ka, nan fa bestie ke shigowa, coz he will be there for her , he’ll cheer her up.. Zai ji matsalolin ta zai ba ta shaw

Matan Arewa

Okkkayyy! Dan anyi maganar kishiya kun fi kowa tada jijiyan wuya. Kece "wayyo Allah, ka cuce ka yaudare ni".. Kwana biyu kuma ki fara "ai ta gama mallake shi".   I'm fed up with "arewa women are not romantic".. Ya tura dan SMS na kara jadadda soyayyar shi a gare ki. Duk rawar ganin da yayi, you can't even reply with "I love you" idan wahalar typing kike. Yasan kin gani kin kuma yaba. Haba! Kiyi laifi ba za ki ce "sorry" ba. Ya yi ma ki kyauta babu "Thank you". Da kin haihu shi kenan ya zama Baban Indo, dan wasa da hirar soyayya kunyi bankwana da su. Da anyi magana ki ce yara. Ko kin girma da haka. In za ki fita kin iya kwalliya da kashe dauri, da kin dawo gida kin kama yawo da zani da shirt, ko daurin kirji. Dare nayi ki haye gado shi kenan. Kin ajiye ma Baban Indo abinci, ya ci ko kar yaci ke dai ai kin girka. Tsakanin ki da mijin ki sai dai maganar kudi "A bani kudin cefane, a bani kudin ankon bik

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. A wannan zamani da mu ke ciki aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa su ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar wannan kalubale. Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai suka iske abun ba haka bane. Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita ciki

DALILAI DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI

DALILAI SHA DAYA DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI Kwanakin baya nayi ta samu korafi daga bakin mata su na kawo kokensu akan miskilan maza. Da yawa na takaicin halayyar irin wadannan mazaje saboda dabi'arsu ta nuna halin ko in kula. Duk da an san cewa dabi'ar mata ce yawan magana, babban rauninsu a rayuwa shine "So", sabili da emotional side dinsu. Inda a maza ba hakan bane, kamar yadda na karanta a cikin littafin "Men are from Mars, Women from Venus", inda na gane bambance-bambance da ke tsakanin mace da namiji. Wasu na ganin cewa miskilanci ra'ayi ne, wani bangaren kuma na ganin halitta ce. Akwai taken da Bahaushe yayi ma miskili "Kafi mahaukaci ban haushi". Ana kallon miskilin mutum a kan cewa mutum ne shi mai girman kai, da jiji da kai, mutum mai wulakanci wanda sam ba haka bane ba. Yanayin halittar shi ce haka ta rashin son magana da kuma shiga abinda bai shafe su ba. Alal hakika ba'a fahimci ya rayuwar miskili take ba, shiyasa da y

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

ALAMOMI GOMA DAKE NUNA CEWA SOYAYYA TA KARE TSAKANIN KI DA SHI Akwai bambanci tsakanin namiji na sonki da kuma bai sonki, wanda zai nuna hakan a aikace, a baki da kuma yanayin mu'amalar ki da shi. Da yawan mata za su fara tunanin ko nayi wani laifi ne? Miye dalilin canzawar shi? Mi ya kamata inyi wajen kara karkato da hankalin shi a gare ni? Ire-iren wadannan tambayoyi ne da za su yi ta yawo a zuciyar budurwar da ta rasa gane kan saurayinta. Wata ba za ta fahimci cewa sonta ne ya daina ba, sai ta fara neman sasanci, ta shiga halin damuwa da tashin hankali musamman idan aka yi sa'ar cewa ta mutu a soyayyar sa. A matsayinki ta mace, wacce aka sani da rauni musamman a bangaren soyayya, ya zama wajibi ki natsu ba'a shiga soyayya ta ka, kin san mi kike so game da namiji sannan ki san alamun da ke nuni da cewa wannan yaudara ce ko kuma an daina yayinki, saboda mune a mafi yawan lokutta muke fadawa ciki. Monica Parikh dake a NYC masaniya akan zamantakewa da soyayya ta bayyan